30 Afirilu 2017 - 17:13
Jagora: Fitowar Al'umma Yayin Zabe Zai Rage Sharrin Makiya Kan Al'ummar Iran

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar fitowar al'ummar Iran kwansu da kwarkwatarsu yayin zabe a koda yaushe yana rage irin makircin makiya a kan su, don haka ya kirayi al'umma da su fito kwansu da kwarkwatarsu yayin zabe mai zuwa wanda shi ma zai rage sharrin makiyan a kansu.

Ayatullah Khamenei, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi dubun dubatan ma'aikatan kasar Iran a daidai lokacin da ake shirin gudanar da bikin ranar ma'aikata ta kasa inda ya ce inda yace: Batun fitowar mutane yayin zabe wani lamari ne mai matukar muhimmanci da zai kara tabbatar da tsaron kasa, don kuwa matukar mutane suka fito to kuwa Iran za ta ci gaba da zama cikin tsaro da kwanciyar hankali.

Haka nan yayin da yake magana kan 'yan takaran da ya kamata a zaba, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar ba zai ce ga wanda za a zaba ba, sai dai ya ce yana kiran al'umma da su fito kwansu da kwarkwatarsu su zabi duk wanda suka ga ya dace. Jagoran ya ci gaba da cewa: Tsoron kasantuwar mutane a fage shi ne babban dalilin da ya sanya makiya suke tsoron wuce gona da iri a kan Iran.

Jagoran yayi watsi da ikirarin da wasu suke yi na cewa shigowarsu fagen siyasa a matsayin dalilin da ya kawar da hatsarin yaki a kan Iran inda ya ce hakan kuskure ne don kuwa kasantuwar mutane a fage shi ne ya kawar da hatsarin yaki da wuce gona da iri a kan Iran.

A ranar 19 ga watan Mayun nan ne za a gudanar da zaben shugaban kasar ta Iran inda aka kimanin mutane miliyan 55 ne suka cancanci kada kuri'unsu inda za su zabi daya daga cikin 'yan takara 6 da suka tsaya ciki har da shugaba mai ci Hasan Ruhani.